Alhazan Nigeria da suka rasu sun kai 99

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wasu daga cikin wadanda suka rasu

Hukumar da ke kula da aikin hajji ta Nigeria ta ce a yanzu adadin 'yan kasar da suka rasu a turmutsitsin da ya faru ranar Idi ya kai 99.

Shugaban hukumar Alhaji Abdullahi Mukhtar Mohammed ne ya tabbatar da wannan adadin a hirarsa da BBC.

"Wadanda suka jikkata sun kai mutane 99 kuma za a samu karin alkaluman wadanda suka rasu nan ba da jimawa ba," in ji Mohammed.

Bayanai sun ce wadanda ba a ji duriyarsu ba a cikin alhazan sun kai mutane 214.

Jihar Sakkwato ita ce tafi yawan adadin wadanda suka rasu a Muna a hanyar zuwa jifan shaidan.

Alhazan wasu kasashe da suka rasu:

 • India 101
 • Pakistan 93
 • Mali 70
 • Bangladesh 63
 • Senegal 54
 • Benin 51
 • Kamaru 42
 • Ethiopia 31
 • Sudan 30
 • Morocco 27
 • Algeria 25
 • Ghana 12
 • Chad 11
 • Kenya 8
 • Turkiyya 3