Kun san sharuɗɗan tantance ministocin Nigeria ?

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sanata Saraki ya ce za su bi ka'ida wajen tantance ministoci

Majalisar dokokin Nigeria ta gindaya sharuɗɗan da za ta bi wajen tantance mutanen da Shugaba Muhammadu Buhari ya aika domin nada su a matsayin ministoci.

Daya daga cikin sharuɗɗan shi ne cewar duk wanda za a tantance sai ya nuna takardar bayanin dukiyar da ya mallaka.

Mai magana da yawun majalisar dattijan, Sanata Dino Melaye wanda ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja, ya kara da cewar dole ne sai sanatoci biyu daga jihar mutum na asali sun amince da shi, kafin majalisar ta amince a nada mutum a matsayin minista.

A ranar Talata, 13 ga watan Oktoba ne, majalisar ta ce za ta soma tantance mutanen.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Fashola na cikin wadanda buhari yake son ya bai wa minista

A makon da ya wuce ne shugaba Muhammadu Buhari ya aike wa majalisar dattijai sunayen mutane 21 domin a tantance su kafin, ya nada su a matsayin ministoci.