'Taba sigari ce ke kashe matasa a China'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Miliyoyin matasa za su mutu a shekarar 2030

Wani sabon nazari ya yi gargadin cewa a nan gaba hayaki ne zai yi sanadiyyar mutuwar mutum daya daga cikin mutane uku 'yan kasar China, idan dai har aka bari shan taba sigari ya ci gaba da zama dabi'ar mutanen kasar.

Nazarin, wanda aka wallafa a wata mujalla mai suna 'The Lancet Medical Journal', ya ce kasar ta China tana fuskantar barazanar karuwar mutuwar matasa masu karancin shekaru.

Binciken ya nuna cewa hakan yana faruwa ne saboda fara shan taba sigari da kaso biyu cikin uku na matasan ke yi tun suna kasa da shekara 20 da haihuwa.

Nazarin ya ce kusan rabin masu shan sigarin tun daga kuriciya za su mutu ne sakamakon hayakin da suke zuka.

Sannan kuma mutane miliyan biyu ne za su rinka mutuwa a kowace shekara idan ba a sanya wa dabi'ar zukar hayakin birki ba daga nan zuwa shekarar 2030.