Boko Haram sun kashe mutane 40 a Chadi

Hakkin mallakar hoto

Ma'aikatan asibiti a Chadi sun ce an kashe mutane kusan 40 wasu fiye da 50 kuma sun sami jikkita a wasu hare-haren bama-bamai uku a kusa da kan iyaka da Najeriya.

Bama-baman sun fashe ne a wata kasuwa da kuma wani sansani na 'yan gudun hijira a garin Baga Sola a gabar Tafkin Chadi.

'Yan Najeriya da dama sun yi kaura zuwa can domin guje wa hare-haren 'yan Boko Haram.

Wani mazaunin garin N'djamena, babban birnin kasar Chadin, ya sheda wa BBC cewa an tsaurara matakan tsaro a birnin.

'Yan kungiyar dai sun cigaba da zafafa kai hare-hare da dama a Chadi da Niger da Kamaru da kuma a cikin Najeriyar kanta.

Karin bayani