'Za mu fara gurfanar da jiga-jigan gwamnati'

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kotun ta ce ba bu wanda zai gagare ta.

Kotun musamman kan da'ar ma'aikata ta ce za ta fara gurfanar da mayan ma'aikatan gwamnati da jiga-jigan 'yan siyasa wadanda suka yi karya ko kuma kin bayyana kadarorinsu, a lokacin da suke kan mukamai.

Shugaban kotun, Danladi Umar ya ce ba bu wani shafaffe da mai da kotun za ta kyale idan dai har ta same shi da laifi.

Ya kara da cewa kotun tasa kawai take iya gurfanar da ma'aikatan gwamnati ko da kuwa shugaban kasa ne.

Dangane kuma da zargin da ake yi wa kotun na rashin gudanar da ayyukanta a baya, Danladi Umar ya ce wannan soki burotso ne domin tun a baya kotun tana aikinta.

A cewar yanzu ne dai kawai hankalin 'yan jarida ya karkata kan ayyukan nata sabanin a baya.

Yanzu haka dai kotun ta gurfanar da shugaban majalisar dattawan kasar, Sanata Bukola Saraki bisa laifin karyar bayyana kadarorinsa a lokacin yana gwamnan jihar Kwara.