Sojoji sun kashe 'yan Boko haram a Gaidam

Sojojin Najeriya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojojin Najeriya

Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce sojojinta sun kashe mafi yawancin daga cikin mayakan Boko Haram da suka kutsa cikin garin Gaidan na jahar Yobe da yammacin ranar Laraba.

Sai dai kuma wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce ta rasa sojojinta uku a lokacin musayar wutar da suka yi da mayakan na Boko Haram.

Rahotannin farko-farko dai sun ce mayakan na Boko Haram sun ci karfin sojojin a arangamar da suka yi a garin, abin da ya ba su damar rike garin har na tsawon dare.

Lamarin da kuma ya mayakan Boko Haram suka fasa wasu shaguna domin kwasar ganima .