Nigeria: Za a yi wa dokokin jihohi garanbawul

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Gwamnonin arewacin Najeriya sun kafa kwamiti don a yi wa dokoki garanbawul

Gwamnonin jihohin arewacin Najeriya sun kaddamar da wani kwamiti na musamman, domin yi wa dokokin jihohin garambawul.

Kwamitin na manyan jami'an shari'a da sakatarorin gwamnati zai yi nazarin yadda za a sabunta dokoki ne domin fuskantar manyan laifuka a yankin.

An kaddamar da kwamitin ne a taron da manyan Alkalan jihohin arewacin kasar ke yi a Kaduna.

Kazalika, dukkan manyan Alkalan da suka halarci taron sun amince cewa dole a sabunta bangarorin shari'ar yankin na arewa mai fuskantar kalubalen tsaro a yanzu.