'Harbin mutane ya zama ruwan dare a Amurka'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Amurka, Obama ya ce dole ne a dakile yawan harbe-harbe

Shugaban Amurka, Barrack Obama ya ce dole ne 'yan kasar su hada kansu domin dakile yawan harbe-harben da ake samu a Amurkar.

Yana magana ne bayan ganawa da iyalan mutanen da aka harbe har lahira a wata kwaleji jihar Oregon a makon da ya gabata a inda wani dalibi ya harbe mutane tara kafin kuma daga bisani ya harbe kansa.

Sai dai kuma kafin tattaunawar, masu rajin kare hakkin amfani da bindiga sun yi wata zanga-zangar limana a filin jirgin saman na Oregon suna masu daga rubuce rubece dake cewa 'ba ma maraba da Obama'.

Akalla mutane biyu ne suka rasa rayukansu a wasu karin jerin harbe-harben da aka yi a jami'o'i da ke jihohin Arizona da Texas na Amurkar ranar Juma'a.