An kashe mutane 95 a harin Turkiyya

Wasu bama-bamai biyu da suka fashe a wani taron gangamin zaman lafiya a tsakiyar Ankara, babban birnin Turkiyya,y sun kashe mutane akalla 95.

Kimanin mutane 200 kuma sun samu raunuka.

Gwamnatin ta yi Allah-wadai da harin wanda ta bayyana a matsayin aikin ta'addanci.

Amma shugaban jam'iyyar HDP mai goyon bayan Kurdawa ya dora laifin ne akan gwamnati.

An dai shirya gangamin zaman lafiyar ne domin a tilasta wa gwamnatin Turkiyyar ta daina kai ma sojin-sa-kan Kurdawa farmaki.

Tuni dai aka bayyana makokin kwanaki uku a Kasar.