Tsohon Gwamnan Bayelsa ya rasu

Hakkin mallakar hoto Unknown
Image caption Tsohon gwamnan ya yi shigar mace ya tsere daga Britaniya a 2005. Zargin da ya karyata

Gwamnan farar hula na farko a jihar Bayelsa, Diepreye Alamieyeseigha yua rasu bayan wata doguwar suma da ya yi a asibiti a ranar Asabar.

Tsohon gwamnan ya rasu ya na da shekaru 63 a duniya.

Gwamnan jihar Dr. Ifeanyi Okowa ya bayyana marigayin da cewa wani babban jigo ne a siyasar jihar wanda mutuwarsa wata babbar rashi ne.

Yayin da danginsa kuma suka bayyana shi da cewa wani gagarumin shugaba ne wanda mutuwarsa ta girgiza su matuka.

A farkon makon nan ne gwamnatin Britaniya ta nuna aniyarta ta a mayar da tsohon gwamnan kasar domin amsa tuhumar da ake yi masa na halarta kudin haram.

An dai taba kama marigayin a watan satumba 2005 a London ne aka kuma gurfanar da shi a gaban kotu a bisa laifin halarta kudin haram, amma da aka bayar da belinsa sai ya tsere a bayan ya yi shigar mace, a inda ya gudo Najeriya, zargin da ya karyata.