Harin bam ya hallaka mutane 9 a Kamaru

Hakkin mallakar hoto
Image caption Mutane tara ne suka mutu a kunar bakin waken

Sojin kasar Kamaru sun ce an kai hare-haren kunar-bakin-wake guda biyu a yankin arewa mai nisa na kasar, kusa da kan iyakar Najeriya.

Hare-haren sun kashe a kalla mutane tara, tare da raunata fiye da 10. Wasu rahotanni sun ce 'yan kunar-bakin-waken mata ne.

Kungiyar Boko Haram dai tana yawan kai hare-hare a yankin, kuma ita aka zarga da kai hari a Cadi ranar Asabar, wanda ya kashe mutane 36.

Sojin Najeriya da na Cadi da Kamaru da Benin da kuma na Nijar suna hada karfi don murkushe masu tada-kayar-bayan.