"Karatun littafai a rediyo na taimaka mana"

Image caption Fauziyya ta rubuta littafai da kuma fina-finai da yawa da Hausa

Wata marubuciyar littafai da fina-finan Hausa Fauziyya D. Suleiman ta bayyana karatun littafan Hausa da ake yi gidajen rediyo da cewa ya taimakawa bunkasar kasuwar littafai.

A hirar da ta yi da BBC marubuciyar ta ce shirin 'Rai dangin goro' na wani gidan rediyo a Kano da ake karanta littafan Hausa ya janyo cece-ku-ce amma ya taimaka wajen fito da littafansu da aka manta da su.

A cewar ta littafan da ta rubuta da dadewa da zaran an karanta su a shirin sai jama'a su bazama neman su, wanda hakan ke sa su sake bugawa.

Sannan littafan ba sa fita kasuwa sai hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta bayar da izini amma duk da haka su na shan suka.

Ta yi kira da malamai da sauran al'umma da su rika karanta littafan su tare da basu shawarwari na gari idan sun yi kuskure.