Jirgin sojin Nigeria ya fadi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Guraguzen wani jirgin sama da ya fadi

Wani jirgin sojin saman Nigeria mai lamba NAF 801 ya fadi a karamar hukumar Hong da ke jihar Adamawa arewa maso gabashin kasar.

Lamarin ya afku ne a yammacin ranar Asabar.

Rahotanni na cewa jirgin ya fado ne a sakamakon mummmunan yanayi kuma matukin jirgin ne kadai ya ya rasa ransa a hatsarin.

Rahotanni na cewa babban hafsan sojin saman Nigeriar ya kafa kwamiti domin gano musabbabin hatsarin jirgin.