Afrika ta Kudu ta janye daga ICC

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Afrika ta Kudu ta ce ICC ta rasa alkibla

Taron sake nazarin manufofi na jam'iyyar ANC mai mulki a Afrika ta Kudu, ya zartar da kudurin janyewar kasar daga Kotun Miyagun Laifuka ta Duniya ICC.

Shugaban kwamitin jam'iyyar a kan harkokin kasashen waje, Obed Bapela, ya ce sun zartar da wannan hukunci ne saboda kotun ta rasa alkiblarta.

An dai soki Afrika ta kudun bisa yin watsi da umurnin kotun na ta mika mata shugaban Sudan Omar Al Bashir, wanda ya halarci taron Tarayyar Afrika a kasar a bana.

Kotun tana nemansa ne bisa zargin laifukan yaki a Darfur.