Amnesty ta bude ofis a Abuja

Image caption Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International a Abuja Nigeria

A ranar Talata ne kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta bude sabon ofishinta a Abuja, fadar gwamnatin tarayyar Najeriya.

Bude ofishin kungiyar a Nigeria ya zama wata sabuwar hanya ga kungiyar da ta yi fice a duniya wajen kare 'yancin dan Adam a yammacin Afirka domin ta fadada ayyukanta a kasar.

A hirarsa da BBC, wani babban jami'in kungiyar mai kula da ofishin, Ambasada MK Ibrahim, ya ce ofishin zai taimaka wajen bunkasa ayyukan kungiyar da kuma kara sa ido a kan ayyukan take hakkin bil adama a kasar.

A baya dai kungiyar ta zargi rundunar sojin Najeriya da take hakkin bil adama a yakin da ta ke yi da 'yan ta da kayar baya na Boko Haram a arewa maso gabashin kasar.