CAF ta fitar da 'yan takarar gwarzon Afirka

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yaya Toure na cikin jerin sunayen da ke yin takara.

Hukumar kwallon kafar Afrika, CAF ta fitar da jerin sunayen 'yan wasa 37 wadanda za su yi takarar "gwarzon dan kwallon Afirka" na shekarar 2015.

Yaya Toure, dan wasan tsakiya na Ivory Coast da Manchester city, wanda shi ne ya lashe gasar a shekarar da ta gabata, ya shiga jerin 'yan wasan da hukumar ta fitar.

Kazalika, an fitar da sunayen Gervinho da Max Gradel da kuma Serge Aurier a matsayin wadanda za su yi takara.

Wasu a cikin jerin sunayen sun hada da Andrew Ayew dan Ghana na Kulob din Swansea City da Ahmed musa dan Najeriya na kulob din CSKA Moscow; Sadio Mane dan Senegal na kulob din Southampton da Pierre-Emerick Aubameyang dan kasar Gabon, na kulob din Borussia Dortmund da Vincent Enyema dan Najeriya na kulob din Lille da kuma Riyad Mahrez dan kasar Algeria na kulob din Leicester city.

Za a ci gaba da tace sunayen mutane 37 din zuwa 10 a watan Nuwamba kafin a kuma ragewa zuwa sunaye biyar, sai kuma a rage zuwa ukun karshe kafin a yi bikin bayyana wanda ya lashe gasar.