Wani ƙusa a China zai sha dauri a kurkuku

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mr Jiemin zai sha dauri

Gidan talabijin na kasar China ya ce an yanke wa tsohon shugaban babban kamfanin samar da man fetur da iskar gasa na kasar, watau Petro - China, hukuncin daurin shekaru 16 a gidan kaso.

Shekaru biyu da suka wuce ne aka kama Jiang Jiemin bisa zargin cin hanci da rashawa.

Masu lura da al'amura sun ce, Mr Min ya kasance hannun damar tsohon shugaban tsaron kasar ne, Zhou Yong-Kang.

Watau mutumin da ke da karfin fada a ji a kasar wanda aka kama da laifin cin hanci, kuma an yanke masa hukuncin daurin rai da rai.

Shugaba Xi Jinping, wanda ya fito da yaki da cin hanci da rashawa na ba sani ba sabo, ya ce wannan wani abin kunya ne ga jam'iyyar Kwaminisanci.