Ana zargin 'yar China da safarar hauren giwa

Hakkin mallakar hoto ap
Image caption An kama wata mata 'yar kasar China a Tanzania da safara hauren giwa.

Wata 'yar kasuwa daga China na neman kotun kasar Tanzania da ta bayar da belinta, bayan ta gurfana gaban kotun kan zargin safarar hauren giwa na kimanin dala miliyan biyu da dubu dari biyar.

Masu bincike sun gano cewar Misis Yang Feng Glan tana da kungiya ta farauta da safarar hauren giwa, duk da cewar tana kasuwancin sayar da abinci da ya bunkasa da kuma noma.

Hukumomin Tanzania sun yi wa Misis Yang lakabi da 'Sarauniyar Hauren giwa' bayan sun shafe shekara suna bincike a kan ta daga bisani kuma suka cafke ta birnin Dar es Salaam a makon da ya gabata.

Ana zargin ta ne da kashe daruruwan giwaye da kuma safarar hauren giwayen sama da 700 cikin shekaru 14 ta haramtacciyar hanya.

Wani rahoto da wata hukumar da ke bincike kan muhallai da ke Amurka, watau Environmental Investigation Agency, ta ce Tanzania ta rasa kashi biyu cikin uku na giwayenta cikin sheakaru goma, an kuma gano cewar Misis Yang tana safarar haure a cikin wannan lokacin.

Idan an same ta da wanna laifin, za a iya mata daurin shekaru 30.