'Yan adawar Guinea sun bukaci a soke zabe

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan adawa sun ce an tafka magudi

'Yan adawar kasar Guinea sun yi kira da a sake gudanar da zaben shugaban kasar da aka yi ranar Lahadi, suna zargin an tabka magudi a wurare da dama.

Babban abokin hamayya, Cellou Dalein Diallo, ya ce mutane na da ikon yin zanga zanga.

Yana magana ne a madadin baki dayan 'yan takarar shugaban kasar bakwai da suka fafata da shugaba mai ci, Alpha Conde.

Hukumar zaben kasar ta Guinea ta ce sai karshen wannan mako za ta bayyana sakamakon zaben.

An kashe mutane da dama a rikicin da ya barke tsakanin magoya bayan gwamnati da na 'yan adawa lokacin yakin neman zaban.