'Yan Nigeria 145 ne suka rasu a Saudiyya

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Har yanzu babu labarin 'yan Nigeria 165 yayinda ake kusan kammala jigilar mahajjata zuwa gida Nigeria

Hukumar kula da aikin hajji ta Nigeria ta bayyana cewa ya zuwa yanzu mutane 145 suka mutu sakamakon turmutsitsin da aka samu a Mina.

Jagororin aikin hajjin kasar sun ce sun fara fitar da ran samun wasu mutanen da ran su daga cikin mutane 165 da har yanzu ba a gan su ba .

Shugaban hukumar aikin hajjin, Alhaji Abdullahi Mukhtar Muhammed shi ne ya tabbatar da wannan adadin a hirarsa da manema labarai a Saudiyya.

Mai martaba Sarkin Kano kuma Amirul Hajjin kasar na bana, Muhammadu Sanusi na II, ya kai wa wasu da suka rasa dangin su ziyarar ta'aziyya.

Sarkin ya ce duk da cewa babu wata hujja da za ta nuna mutanen da ba a gani ba sun mutu, amma ya ce an bi duk wata kafa da za a iya gano mutanen amma babu duriyar su.