Buhari ya aika karin sunayen ministoci

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Saraki ne zai jagoranci tantance ministoci

Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya aike wa majalisar dattijan kasar karin sunayen mutanen da ya ke so ya nada a matsayin ministoci.

Babban ma'aikaci a fadar shugaban kasar, Alhaji Abba Kyari da masu bai wa shugaban kasa shawara a kan harkokin majalissun dokoki, Sanata Ita Enang da kuma Alhaji Kawu Sumaila su ne suka mika wasikar shugaban kasar kunshe da sunayen, ga shugaban majalisar dattawa, Sanata Abubakar Bukola Saraki.

Wannan ne kashi na biyu na jerin sunayen da fadar shugaban kasar ta aike wa majalisar dokokin kasar.

A ranar 30 ga watan Satumba ne, Shugaba Buhari ya aike wa majalisar sunayen mutane 21 domin ya nada su a matsayin ministocin Nigeria.

Tuni shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki ya bayyana ranar Talata, 13 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za a soma tantance ministocin.

Daga cikin sunayen da ke jerin farko akwai tsofaffin gwamnoni da kuma masana a fannoni daban-daban.