IS ce ta kai hari a Ankara - Davutoglu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mr Ahmet Davutoglu ya ce IS ce ta kai hari a Ankara a karshen makon jiya.

Firai Ministan Turkiyya, Ahmet Davutoglu , ya yi zargin cewa kungiyar IS da ke ikirarin kishin Musulinci ce ta kai hari a wajen wata zanga-zanga a birnin Ankara ranar Asabar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 100.

Babu dai wata kungiyar da ta dauki alhakin kai hare-haren, amma gwamnatin kasar ta yi amannar cewa wasu maza biyu 'yan kunar-bakin-wake ne suka kai shi.

Alkaluman da gwamnati ta fitar sun nuna cewa mutane 97 suka mutu sakamakon hare-haren, sai dai daya daga cikin kungiyoyin da suka hada zanga-zangar ta ce mutane 128 suka mutu.

A ranar Litinin ne dai ake yin jana'izar mutanen da suka mutu.