Zargin maita na karuwa a Biritaniya

Hakkin mallakar hoto Getty images

Alkaluma da BBC ta samu sun nuna cewar cin zarafin yara wadanda ya danganci rukiya da zargin maita yana karuwa.

'Yan sandan Biritaniya sun ce akwai laifuka 60 wadanda aka aikata kuma suke da alaka da addini da aka aikata a London a shekarar 2015.

Rahotannin da aka fitar na shekarar 2013 sun nuka daga 23 zuwa 46 a shekarar 2014.

Rabin 'yan sandan Ingila ba sa ajiye rahotannin irin wadannan laifuka kuma hukumomin kasar ma basa iya bayar da alkaluma.

Kungiyar kare cin zarafin yara ta NSPCC ta ce ya kamta hukumomi "su iya gane alamomin wannan nau'in cin zarafi."

London na da jami'an 'yan sanda na musamman da aka kebe domin kula da irin wannan nau'in cin zarafin.

Alkalumansu suna da alaka da rahotannin laifuka inda jami'ai suka maida hankali a kan wani laifin wanda ya danganci cin zarafin da ya ke da alaka da addini ko wata akida.

Mafi yawan wadannan laifukan sun shafi yara ne.

Labarin Ibidapo: "Na ji tamkar bani da muhimmanci"

Hakkin mallakar hoto Getty images

An yi safarar Ibidapo zuwa Ingila ne a shekarar 2007, domin ta yi aiki a gidan wasu 'yan uwanta a arewacin Ingila.

Sun zarge ta da maita sannan suka hana ta zuwa makaranta kuma suka rika azzabtar da ita.

Amma kuma ta samu ta tsere da taimakon makwabciyarsu 'yar Najeriya.

Ta ce "Shekaru na 10 da haihuwa a lokacin da na fara zama da 'yar uwa ta, domin na taimaka mata wajen kula da jaririnta. Idan ta fita aiki, sai a bar ni da jinjirin, ni na ke yin aikace-aikacen gidan har da wanki da ma girki."

Alkaluman da BBC ta samu ta hanyar amfani da dokar bai wa 'yan jarida bayanai sun nuna cewar rabin 'yan sandan Biritaniya ba sa ajiye bayanan irin wadannan laifukan a kai a kai.

'Kora daga gida'

Wannan na faruwa duk da wata shawara da gwamnatin Biritaniya ta bayar a wani rahoto na cewar laifukan da suke da alaka da zargi na aljannu ko kuma maita a ajiye bayanai a kansu.

Debbie Ariyo, shugabar kungiyar yaki da cin zarafin yara ta 'African unite Against Child Abuse' ta ce mafi yawan lokuta ana zargi ne idan iyalai suka fara fuskantar matsaloli:" Ana dorawa yara alhaki - musamman idan 'yan uba ne."

'Rashin sani'

Hakkin mallakar hoto Getty images

Ta yi gargadin cewar, a dai na yi wa lamarin kallon wani abu ne da ya ke damun 'yan Afrika kadai, saboda kungiyar ta, ta taimakawa wadanda abin ya shafa daga addinai daban-daban da kuma al'adu daban-daban wadanda suka hada da al'ummar 'yan kudancin Asiya.

Ta damu da rashin sannin afkuwar wadannan laifuka ga kwararru wajen kula da yara a Biritaniya.

'Azabtarwa mai tada hankali'

Wani mai magana da yawun kungiyar kare yara daga azabtarwa ta NSPCC ya ce: Yayin da laifukan cin zarafin yara wadanda suka kunshi maita basu da yawa sosai, a lokuta da dama akwai azabtarwa mai daga hankali.

"Ya kamata hukamar da ke kula da irin wadannan munanan laifukan, su tabbatar suna iya gano alamomin irin wannan nau'in cin zarafin kuma su dauki mataki domin kare yara kafin wani tashin hakalin ya faru."