Bam ya hallaka mutane bakwai a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto Screen Grab
Image caption 'Yan kunar bakin waken sun tayar da bama baman ne a wurare daban-daban.

Wasu mutane da ake zargin 'yan kunar bakin wake ne sun tayar da bama-bamai a Maiduguri da ke jihar Bornon Najeriya a daren Talata.

Ganau sun shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne a yankuna daban-daban.

Shi ma kakakin rundunar sojan kasa ta Najeriya, Kanar Usman Kuka Sheka, ya tabbatar wa BBC aukuwar lamarin, yana mai cewa 'yan kunar bakin wake uku ne suka kai hare-haren a wurare daban-daban a unguwar Ajilari.

Hukumomin soji a Nigeria sun tabbatar da mutuwar mutane bakwai suka halaka sannan mutane goma sha daya suka sami raunkuna.

A cewar sa, 'yan kunar bakin waken sun tayar da bama-baman da ke jikinsu kimanin mintina uku tsakanin juna.

Mutane kusan 150 aka kashe ko kuma aka jikkata a fashewar wasu abubuwa irin wannan a Maiduguri, makonni hudu da suka gabata.

Ya kara da cewa mutane bakwai ne suka mutu -- cikin su har da maharan -- sannan mutane 11 suka jikkata.

Wannan harin ya zo ne a lokacin da rundunar sojin Najeriya ke ikirarin samun nasara a kan kungiyar Boko Haram.