Yunwa ta addabi al'ummar Habasha

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Galibin 'yan Habasha sun yi fama da fari a 2011

Gwamnatin kasar Habasha ta ce sama da mutane miliyan takwas na bukatar tallafin gaggawa na abinci sakamakon fari da ake fama da shi a kasar.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce wannan ya fi linkin adadin da ke bukatar abincin watanni biyun da suka wuce.

Dubban kananan yara na fama da tsananin yunwa, yayin da dimbin dabbobi suka mutu sakamakon rashin ruwan sama damina biyu.

Duk da cewa Habasha na daya daga cikin kasashen da tattalin arzikinsu ke habaka nan da nan, kasar na ci gaba da fuskantar karancin abinci.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin wadanda abin zai shafa zai kai miliyan 15.