Makami mai linzami ne ya harbo jirgin MH17

Hakkin mallakar hoto Reuters

Wani bincike da kasar Netherlands ta gudanar dangane da harbo jirgin Malaysia Airline a Ukraine watan Yunin da ya gabata, ya karkare cewa jirgin kirar Boeing 777 wani makami mai linzami kirar Rasha ne ya kakkabo shi.

Da ya ke magana a wani sansanin jiragen sama na Netherlands, shugaban kwamitin binciken, Tjibbe Joustra, ya ce gwaje-gwajan da aka yi sun nuna cewa wani makami mai linzami kirar BUK 6 ya tarwatse kimanin mita daya ta wajen matukin jirgin.

Ya ce ya kamata a ce Ukraine ta rufe sararin samaniyarta ga jiragen da ba na yaki ba, inda ya kara da cewa a lokacin a kwai wasu jirage uku da ke dab da wajen.

Da yake mai da martani ga rahotan kwamitin binciken, Firai ministan Netherlands, Mark Rutte, ya yi kira ga mahukuntan Rasha da su bada cikakken goyan bayansu ga binciken da ake gudanarwa na wanda ke da hannu a kakkabo jirkin saman na Malaysia.

Mr Rutte ya kwatanta binciken kan abin da ya faru a matsayin wani babban abin da ya tasiri a kan dangantakar da ke tsakanin Holland da Rasha.