Sanatoci sun tantance ministoci 10

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sanata Saraki ya ce babu nuna bambanci a wajen tantance mutanen

Majalisar dattijan Nigeria ta tantance mutane 10 daga cikin 37 da shugaba Muhammadu Buhari ya ke son ya nada a matsayin ministoci.

Majalisar karkashin jagorancin, Sanata Abubakar Bukola Saraki ta gayyaci mutanen daya bayan daya domin amsa tambayoyi kan rayuwarsu da kuma irin ayyukan da suka yi.

An soma ne da Sanata Udoma Udo Udoma daga jihar Akwa Ibom wanda bayan ya gabatar da kansa sai aka ba shi damar ya rusunawa 'yan majalisar sannan ya kama gabansa.

Sauran wadanda aka tantance a zaman farko a ranar Talata sun hada da; Kayode Fayemi daga jihar Ekiti, da Audu Ogbeh daga jihar Benue da Ogbonayya Onu daga jihar Abia da kuma Osagie Ohanire daga jihar Edo.

Tsohon babban hafsan sojin kasa na Nigeria, Laftar Janar AbdulRahman Dambazau daga jihar Kano da Kakakin jam'iyyar APC na kasa, Alhaji Lai Muhammed da kuma Hajiya Amina Mohammed 'yar jihar Gombe na daga cikin mutanen da suka bayyana gaban majalisar.

Injiniya Sulaiman Adamu daga jihar Jigawa da kuma Alhaji Ibrahim Usman Jibrin daga jihar Nasarawa su ne mutane na karshe da suka bayyana gaban majalisar kafin ta dage zamanta.

Ana sa ran a ranar Laraba majalisar dattawan za ta koma zamanta domin ci gaba da tantance mutanen da ake son a nada ministocin.

Jerin wadanda aka tantance:

  • Sanata Udoma Udo Udoma daga jihar Akwa Ibom
  • Kayode Fayemi daga jihar Ekiti

  • Audu Ogbeh daga jihar Benue
  • Ogbonayya Onu daga jihar Abia

  • Osagie Ohanire daga jihar Edo

  • Laftar Janar AbdulRahman Dambazau daga jihar Kano
  • Alhaji Lai Muhammed daga jihar Kwara
  • Hajiya Amina Mohammed daga jihar Gombe

  • Injiniya Sulaiman Adamu daga jihar Jigawa
  • Alhaji Ibrahim Usman Jibrin daga jihar Nasarawa