'Yan gudun hijirar Syria na komawa gida

Image caption 'Yan syria na cikin matsanancin hali.

Cikin kuka 'yan kasar Syria ke ban kwana da juna a arewacin Jordan, inda yara ke taimakawa iyayen su da sanya kaya a mota da ke jira ta tafi da su.

Wadannan 'yan gudun hijirar ba su da halin zuwa Turai, wasu kuma ba sa son zuwa ne kurum, sun dau niyyar wata tafiya ce mai hadari na komawa kasar su inda yaki ya daidaita.

"Ba ni da dangi a nan, ga shi ina fama da rashin kudi," In ji wata mahaifiyar yara uku daga Deraa da ke Syria ta kudu.

"Duk an gaji ana ta tafiya gida, babu komai ay tunda nan zaka samu 'yanuwa, kuma duk abunda zai faru ya faru"

Image caption Halin da 'yan Syria ke ciki a kasar Jordan ya tilasta masu yanke shawara komawa kasar su.

A cikin makonnin nan, Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta damu da yadda 'yan gudun hijira ke komawa Syria, inda a watan Yuli ta kiyasta cewa kimanin 'yan gudun hijira 66 ne suke koma wa a duk rana, amma a watan Agusta alkaluman ya rubanye har zuwa 129, gabannin haka kuma ake samun sama da mutane 100 a kowace rana.

Akwai 'yan gudun hijira sama da 600,000 daga Syria da ke zaune a Jordan, kuma yawancin su na zauna cikin matsanancin halin talauci da rashin muhalli a biranen kasar.

'Hanya daya'

Hakkin mallakar hoto none
Image caption Kusan 'yan gudun hijira 4,000 ne suka dawo Syria a watan Agosta, wannan alkaluman ya rubanya na watan baya.

Dole wadanda ke neman komawa Syria su yi rajista a tashar bas bas da ke Zaatari, wani sansanin 'yan gudun hijira, kuma sashen da ke kula da 'yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya, watau UNHCR, na bai wa wasu daga cikin su shawarwari.

"Abu na farko da muke gaya masu shi ne babu kwanciyar hankali a Syria, sannan kuma idan sun koma ba za su iya dawowa Jordan ba, hanya daya ce," In ji Omar, wani jami'in UNHCR.

'Yan gudun hijiran Syria da ke Jordan na cikin mawuyacin hali, inda Majalisar Dinkin Duniya ta ce kaso 86 cikin 100 cikin su na zama ne cikin talauci.

'Tsaka mai wuya'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mayakan sa kai a Syria, watau Free Syrian Army (FSA) suna na shirya wa farmakin da Rasha ke shirin kaiwa kasar.

Gwamnatin Jordan ta sa dokar hana aiki kuma ta soke bayar da kula na asibiti, hakan ya sa iyalan 'yan gudun hijira da yawa suka yanke shawarwar masu ban takaici.

Wani dan gudun hijira Abu Ahmed, daga garin Homs ya ce dole ta sa ya zauna da mahaifiyarsa, kuma ya tura matarsa da yaran su kanana mata biyu garin Damascus, wurin iyayen matar ta sa.

Ya ce "Wannan rayuwa akwai wahala, yarinya ta bata da lafiya, bani kuma da halin kai ta asibiti a nan. Na san za ta samu kulawa a Syria."

Mayakan sa kai a Syria da ke kiran kansu Free Syrian Army (FSA) sun ce suna bukatar karin makamai domin kare al'umma, amma kuma shigowar da Rasha ta yi kasar zai kara yawaita kashe-kashe ne.

Kakakin kungiyar FSA da ke kudu, Manjo Issam al-Reis ya ce "Lamarin ya kara hargitsewa, ana yawaita kawo farmaki da hare-haren bam da ke kashe fararen hula, don haka muke bai wa 'yan gudun hijira shawarar kar su dawo Syria, saboda akwai hadari."