Twitter zai rage ma'aikata 330

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kamfanin Twitter ya sanar cewar zai sallami ma'aikatansa 330 daga bakin aikinsu.

Ayyukan da Twitter zai rage ya shafi kashi takwas na ma'aikata ta na duniya.

Mafi yawan ayyukan da aka rage sun shafi Injiniyoyi ne.

A watan Yulin shekarar 2015 ne, Twitter din ya bayyana cewar yawan mutane da ke amfani da dandalin sada zumuntar a duk wata ya yi kasa sosai tun da mutane suka fara amfani da dandalin a shekarar 2013.

Sanarwar ta zo ne mako guda bayan an nada mataimakin shugaban kamfanin, Jack Dorsey, a matsayin sabon shugaba na dindindin.

A wani sako da ya aike wa ma'aikatansa, Mr Dorsey ya ce Twiter zai fi samun ci gaba da wuri da ma'aikata kadan.