Buhari ya janye sunan Ahmed Ibeto

Image caption Shugaba Buhari bai fadi dalilin janye sunan Musa Ibeto ba.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya janye sunan daya daga cikin mutanen da ya aikawa majalisar dattawa domin nada su ministoci.

Shugaban majalisar dattawan, Bukola Saraki ne ya sanar da wannan mataki a ranar Laraba.

Sai dai bai bayyana dalilin da ya sa Shugaba Buhari ya janye sunan Ahmed Musa Ibeto daga cikin mutanen da za a nada ministocin ba.

Sai dai a cikin sunaye 37 da Shugaba Buhari ya tura majalisar dattawa domin tantancewa, akwai mutane biyu da suka fito daga jihar Niger.

Alhaji Ibeto dai tsohon mataimakin gwamnan jihar Niger ne kafin zabukan shekara ta 2015, kuma ya raba gari da gwamnansa saboda sauya sheka zuwa jam'iyyar APC ta shugaba Buhari a bara.

A ranar Laraba ne ake ci gaba da tantance mutane 37 da shugaban ya aikewa majalisar domin tantance su.

A ranar Talata aka tantance mutane 10, cikin su har da tsohon gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi da Abdurrahman Dambazau da Amina Mohammed da sauran su.