China ta bullo da tsarin kautata wa iyaye

Hakkin mallakar hoto AP

A kasar China, an bullo da wani tsari da za a tilasta wa ma'aikata bai wa iyayensu kashi goma cikin dari na albashinsu.

Dokar -- wacce wani kamfanin kasar ya bullo da ita -- ta jawo muhawara a shafukan sada zumunta a kan yadda ya kamata a rika tausaya wa iyaye ko wadanda suka manyanta.

Jaridar Guangzhou Daily ta rawaito cewar kamfanin, wanda wani wurin gyaran gashi ne da ba a bayyana sunan sa ba, ya bullo da wannan manufar ne domin samar da kyawawan dabi'u ga ma'aikatansa.

Ana daukar wannan mataki a matsayin girmama wa iyaye a kasar ta China.

Amma kuma, labarin wanda kafafen yada labarai da dama suka rawaito, ya jawo tattaunawa a kan ko kamfanin ya tsaurara wa ma'aikatansa da yawa.

Akasarin iyaye a China suna sa ran 'ya'yansu su ba su wani kaso daga albashinsu da zarar sun fara aiki.

A shekarar 2013 ne China ta kaddamar da wata doka da manufar karfafa tausayi ga iyaye ko wadanda suka manyata, inda ta wajabta cewar dole ne wadanda ba sa zaune tare da iyayensu su rika kai musu ziyara a kai a kai.