'Alhazai 1,620 ne suka rasu a Saudiyya'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kasashe sun soki yadda Saudiyya ke lura da batun wadanda suka rasu

Adadin mutanen da suka rasu a turmutsutsun da aka yi lokacin aikin hajjin bana a Saudiyya ana tsammanin yanzu ya kai akalla mutane dubu daya da dari shida da ashirin.

An dai samu wannan adadin ne daga jami'an harkokin wajen kasashen da suke da mutanen da suka je aikin hajjin na bana.

Wannan dai ya kasance hadari mafi muni da aka taba samu a lokacin aikin hajji a tarihi.

Adadin da ma'aikatar lafiya ta Saudiyyan tabayar dai dari bakwai da sittin da tara ne.

'Yan Nigeria 168 ne hukumomin kasar suka ce sun rasu sakamakon hadarin na ranar Idi.