Cin hanci: An kori 'yan sanda 63 a Kenya

Image caption An gano cewa kananan 'yan sanda na aikawa manyan su kudaden da suka karba a matsayin cin hanci.

Hukumar kula da 'yan sandan Kenya ta kori manyan jami'an 'yan sandan kasar 63 saboda samun su da hannu a karbar hanci.

Hukumar ta ce ta dauki matakin ne bayan ta kwashe watanni 14 tana gudanar da bincike a kan 'yan sanda 1,400.

A cewar ta, akasarin 'yan sandan da aka kora daga aiki, suna aiki ne a sashen bai wa ababen hawa hannu na hukumar.

Shugaban hukumar, Johnston Kavulundi, ya ce a lokacin da suke yin binciken sun gano kananan 'yan sandan da ke bai wa ababen hawa hannu suna sanya kudade a kai-a kai a asussan ajiyar kudaden manyan 'yan sandan.