Ban san ranar komawa Sudan ta Kudu ba — Machar

Hakkin mallakar hoto Reuters

Tsohon mataimakin shugaban Sudan ta Kudu Riek Machar ya ce bai san lokacin da zai koma kasar domin ya ci gaba da aiki ba.

Karkashin sharuddan wata yarjejeniyar zaman lafiya da aka sanya wa hannu a watan Agusta, Mr Machar zai koma Sudan ta Kudu a watan gobe domin yin aiki tare da Shugaba Silva Kiir.

Amma Mr Machar ya ce zai koma kasar ne kawai idan aka ba shi tabbacin tsaron lafiyarsa.

Machar ya samu sabani da Shugaba Salva Kir jim kadan bayan kasar ta samu 'yancin kanta a shekarar 2011, kuma yakin basasa ya barke, abin da ya sa ya fice daga babban birnin kasar na Juba a watan Disambar shekarar ta 2011.