An sace Fan miliyan 20 ta intanet a Birtaniya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana amfani da manhajar Dridex wajen satar kudi a Birtaniya

Hukumar hana laifuka ta Birtaniya tana farautar wasu mutane wadanda suka sace tsabar kudi har Fan miliyan 20 daga bankunan kasar ta Birtaniya, ta kafar intanet.

Yanzu haka hukumar ta ce tana aiki tare da hukumar FBI da sauran hukumomin tsaro domin hana yin amfani da manhajar da take ba wa masu laifi damar satar wa mutane kudade, mai suna Dridex.

Hukumar ta NCA ta kara da cewa ta samu nasarar cafke wani mutum guda da ake zargi da aikata satar kudin ta manhajar Dridex.

Ana amfani da wannan manhaja ta Dridex ne domin samun bayanai akan masu ajiya a bankuna har ma kuma a yashe musu 'yan kudaden nasu.

Ita wannan fasahar tana shafar komfuta ne ta hanyar amfani da shafin rubutu Microsoft Office document da ake aika wa masu komfuta a zuwan takardar shaidar saye da sayarwa, ta kafar email.

Mutane kuma su kan makala sakon da aka aiko musu a komfutarsu ba tare da sun bincika ingancinta ba.

Da zarar an makala manhajar a kan komfuta za ta fara aika bayanai da suka kunshi lambobin sirri da asusun da mutane suke ajiyar kudadensu, zuwa wadanda suka aiko da manhajar.

Wani kwararre kan harkar tsare intanet, farfesa Alan Woodward ya shaida wa BBC cewa masu amfani da manhajar suna da matukar wayo ta hanyar yin takatsantsan domin ka da a gano su.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu satar suna aika wa mutane manhajar Dridex zuwa komfutoci ta hanyar email

Farfesa Alan ya ce " wannan wata manhaja ce wadda ake amfani da ita wajen leken asirin bayanan mutanen da ba sa kaffa-kaffa da bayanansu".