An dakatar da shugabar 'yan sandan Afrika ta Kudu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Phiyega na shan suka

Shugaban Afrika ta Kudu, Jacob Zuma ya dakatar da shugabar 'yan sandan kasar Riah Phiyega domin a binciki yadda ta gudanar da aikinta.

Tuni aka kafa wani kwamiti domin duba yadda lamaru suka kasance har aka kashe mutane a 2012

Kwamitin binciken zai binciki yadda ta tafiyar da shugabancinta wanda ya yi sandiyar mutuwar masu aikin hako ma'adanai 34 da 'yan sanda suka kashe a Marikana a shekarar 2012.

A yayin da shugaban kasar ya bayar da wannan sanarwa, rahotanni sun ce shugabar hukumar 'yan sandan na zauren majalisar dokokin kasar inda take gabatar da rahoton hukumar na wannan shekarar.

Dama dai an dade ana yin kiraye-kiraye na a cire Janar Phiyega daga mukaminta.