Boko Haram: Amurka ta tura sojoji 300 Kamaru

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Amurka ta lashi takobin kawo karshen Boko Haram

Shugaban Amurka, Barack Obama ya ce kasarsa ta tura dakarun soji 300 zuwa kasar Kamaru domin yaki da kungiyar Boko Haram.

A wata sanarwa da ta fito daga fadar gwamnatin Amurka, Mr Obama ya ce dakarun za su dukufa ne wajen tattaro bayanan sirri da yin cikakken bincike a kan yadda ake tsara hanyoyin da za su kawo karshen hare-haren Boko Haram.

A cewar sa, tuni dakarun kasar 90 suka isa kasar ta Kamaru.

Ya kara da cewa dakarun za su ci gaba da zama a Kamaru har sai sun tabbatar "ba a bukatar su".

Kungiyar Boko Haram ta addabi kasashen Kamaru da Chadi da Nijar da kuma Najeriya inda ta hallaka mutane fiye da 15,000 a cikin shekaru shida.

Kasashen tafkin Chadi dama suna neman taimakon manyan kasashen duniya domin kawar da kungiyar Boko Haram.

Hakkin mallakar hoto Screen Grab

Tuni kungiyar Boko Haram ta yi mubaya'a ga kungiyar IS mai ikirarin kafa daular musulunci.