Tsohon Shugaban Benin Kerekou ya rasu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mathiue Kerekou shi ne shugaban kasar Afrika na fari da ya amince da shan kaye a zabe, a shekarar 1991.

Tsohon shugaban kasar Benin, Mathieu Kerekou wanda ya yi fice wurin jaddada dimokradiyya a nahiyar Afrika, ya rasu yana da shekaru 82.

Mista Kerekou ya hau karagar mulki tun shekarar 1972, inda ya yi mulkin kasar sau biyu a shekaru kusan 30.

Daga bisani bayan ya amince da dimokradiyya, wacce ta tanadi tsarin jam'iyyoyi da dama, sai ya sha kaye a zaben shekara 1991.

Tsohon shugaban, shi ne na farko cikin shugabannin Afrika da ya amince da kayen da ya sha a zabe.

Shugaban kasar na yanzu Thomas Boni Yayi, ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai kwar jini, kuma ya bayar da mako guda a kasar domin alhinin rashin.