Za a janye motocin Volkswagen a Jamus

Hakkin mallakar hoto afp

Gwamantin Jamus ta ce za ta tilastawa kamfin kera motoci na Volkswagen ta janye motoci fiye da miliyan 2 da ake gani suna cikin badakalar nan ta fitar da hayaki mai gurbata yanayi.

Alexander Dobrindt, ministan sifiri na kasar, ya ce za a fara janye motocin ne a watan Janairun badi.

Kamfanin Volkswagen din yana ganin kusan motocinsa miliyan 11 a duniya masu amfani da man diesel suke da matsalar ta naurar hayaki.

Suna san ran wasu daga cikin motocin za su bukaci gyaran naura ce kawai wanda za a iya cikin sauki.

Mr Donald ya kara da cewar wasu kuma zasu bukari gyara sosai wanda baza a gama ba sai wata shekarar.