Kuna wanke hannu idan za ku ci abinci?

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mutane dubu 97 ne ke mutuwa a Najeriya saboda rashin wanke hannu.

Masana kiwon lafiya sun ce wajibi ne jama'a su dauki dabi'ar wanke hannu da muhimmanci domin rage mace-mace sakamakon cututtukan da kazanta ke haifarwa.

Alkaluma sun nuna cewa kimanin yara dubu 97 ke mutuwa a kowacce shekara a Najeriya sakamakon kazanta da rashin tsaftataccen ruwa.

Masana kiwon lafiya dai na ganin cewa da dama daga cikin jama'ar kasar ba su damu da karfafa wanke hannu musamman ga yara kanana.

Cututtukan da masanan suka ce ana kamuwa da su sakamakon rashin dauraye hannu su ne Ebola da amai da gudawa da cutar numoniya da sauransu.

Wata kungiyar kasa da kasa mai fafutikar ganin ana wanke hannu da sabulu ta sanya ranar 15 ga watan Octoban kowacce shekara ta zamo ranar wanke hannu ta duniya.

A irin wannan rana dai ana tunatar da gwamnatoci da al'umma kan amfanin wanke hannu da kuma irin cututtukan da rashin wankin ke haifarwa.