Mutane 39 sun hallaka a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto Screen Grab
Image caption 'Yan Boko Haram sun je babu gudu babu ja da baya

Jama'a a Maiduguri babban birnin Jihar Borno na ci gaba da zaman jimami bayan wasu hare-haren da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 39.

Baya ga hare-haren da aka kai a wani masallaci a daren Alhamis, a ranar Juma'a kuma wasu 'yan kunar bakin wake uku sun yi sanadiyar hallaka mutane hudu a garin Mule da ke bayan birnin na Maiduguri.

Babban jami'in hukumar agajin gaggawa NEMA, Muhammad Kanar wanda ya tabbatar wa BBC wannan adadin na wadanda suka rasu, ya ce har yanzu ba a kai ga tantance yawan mutanen da suka samu raunuka ba sakamakon hare-haren.

A ranar Alhamis, an kai harin ne a wani Masallaci a unguwar Mola da ke birnin Maiduguri lamarin da ya janyo rasuwar mutane akalla 30.

'Ganau'

Wani ganau ya shaida wa BBC cewa mutane biyu ne suka je masallacin bayan an fara sallar Magriba a inda na farko ya tayar da bam a cikin masallacin.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakaru sun yi ikirarin samun nasara

A cewar sa, mutum na biyun wanda yake wajen masallacin ya tayar da bam din da ke jikinsa a lokacin da mutanen da ke waje suka yi kokarin kai wa mutanen da ke cikin masallacin dauki.

Ko a daren ranar Talata ma 'yan kunar bakin wake sun tayar da bama-bamai a unguwar Ajilari inda mutane bakwai ne suka mutu sannan mutane 11 suka jikkata.

Mutane kusan 150 aka kashe ko kuma aka jikkata a fashewar wasu abubuwa irin wannan a Maiduguri, makonni hudu da suka gabata.

Wannan harin ya zo ne a lokacin da rundunar sojin Najeriya ke ikirarin samun nasara a kan kungiyar Boko Haram.