An dage tantance ministocin Nigeria

Hakkin mallakar hoto Nigeria Senate
Image caption Wasu daga cikin ministocin da aka amince da su

Majalisar dattawan Nigeria ta dage tantance mutanen da Shugaba Muhammadu Buhari ya nada su a matsayin ministoci zuwa ranar Talata.

Majalisar ta bayyana haka ne a sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter.

Ba ta fadi dalilin dage tantance ministocin ba.

Gabanin dage zaman tantance ministocin na yau, 'yan majalisar sun amince da ministoci 18 da suka tantance ranar Laraba.

Kazalika, 'yan majalisar sun jinkirta tantance tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Ameachi zuwa ranar Alhamis.

Matakin ya biyo bayan rashin mika rahoton kwamitin da'a da korafe-korafen jama'a na majalisar dattawan da ke binciken wani korafi a kan Mr Amaechi.

Shugaba Muhammadu Buhari ya aike wa majalisar sunayen mutane 37 ne domin ya nada su a matsayin ministoci ko da ya ke daga bisani ya janye sunan Alhaji Ahmed Ibeto daga jihar Niger.

Ana ganin an janye sunan sa ne saboda an aike da sunayen mutane biyu daga jihar zuwa majalaisar ta dattawa.