Tesla ya fito da mota maituka kanta

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Motocin za su iya sauya hannu da rage gudu da kansu

Kamfanin kera mota na Tesla ya fito da wata fasahar zamani da za ta ba wa motocin kirarsa damar tuka kansu.

Duk da cewa ba wai za su tuka kan nasu kai tsaye ba ne amma ita fasahar da aka sanya wa motocin kamfanin samfirin Model S da Model X, za ta ba su damar tuka kansu akan manyan tituna da sauya hannu da kuma rage gudu a cikin turmutsutsun motoci.

Shugaban kamfanin Tesla, Elon Musk ya ce an fito da fasahar da za ta ba wa mota damar tuka kanta ne domin kara wa direbobi karfin gwiwa yayin tuki a kan tituna.

Sai dai kuma mista Musk din ya gargadi masu direbobin motocin samfirin Model S da Model X da su yi a hankalai yayin amfani da fasahar.

Ya ce " ayi takatsantsan ka da a ture masu tafiya da kafa".

Mista Musk ya kara da cewa idan motar mai dauke da fasahar ta samu kanta a hadarin taho mu gama da wata motar to laifin direban ne. Yanzu haka kamfanin ya fito da ita wannan fasahar a arewancin Amurka. Kuma nan ba da jimawa ba za a fito da fasahar a sauran sassan duniya.

Fasahar dai tana amfani da na'urar daukar hoto ta kamera da dai sauran na'urori da suke gano taswirar wurare.

Hakkin mallakar hoto
Image caption Motocin kuma za su fi yin aiki ne a kan manyan tituna

Ita dai wannan motar tana yin amfani da na'urorin domin gano wurin da za ta yi fakin.