Turai ta cimma matsaya kan 'yan gudun hijira

Hakkin mallakar hoto bbc

Shugabannin Tarayyar Turai da suke tattauna wa a Brussels sun ce sun cimma matsaya kan shirin da suke yi na neman tallafin kasar Turkiyya da nufin magance matsalar shigar 'yan gudun hijra zuwa Turai.

Shugaban hukumar tarayyar Turai, Jean-Claude Juncker ya ce yanzu haka Turkiyya ta yarda ta hana 'yan hijrar da ke kasarta kwarara zuwa Turai a kan tsarin ban-gishiri-in-ba-ka-manda.

A nata bangaren, Tarayyar Turai ta yi alkawarin bayar da takardun izinin shiga cikin ta ga 'yan kasar ta Turkiyyar ba tare da tsangwama ba.

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, ta ce Tarayyar Turai tana duba yiwuwar bai wa Turkiyya tallafin Yuro biliyan uku domin daukar dawainiyar 'yan gudun hijirar kasar Syria da ke zaune a Turkiyyar.