Fela: Ana tuna ranar haihuwarsa

Image caption Margayi Fela a lokacin yana cashewa

Masu sha'awar salon kida da waka na 'Afrobeat' a duk fadin duniya na ci gaba da bukukuwan tunawa da ranar haihuwar fitaccen mawakin nan Fela Anikulapo Kuti, wanda ya rasu a shekarar 1997.

Yanzu dai shekaru 77 kenan tun bayan haihuwar Fela, wanda ya yi tasiri sosai wajen yin wakoki da ke tabo batutuwan talauci da cin hanci da rashawa da kuma rashin adalci a Najeriya.

Wasu daga cikin wakokinsa da suka fi yin fice sun hada da 'Zombie' wadda ya fitar a shekarar 1976. Wakar ta yi kakkausar suka ga sojan Najeriya.

Sauran wakokinsa da suka yi fice sun hada da 'Shakara' da kuma 'Expensive shit' da kuma 'Shuffering and Smiling' wadda ta tabo wahalar rayuwa da 'yan Najeriya suke fuskanta yau da kullum.

Fela dai yayi tasiri sosai a fagen waka a ciki da wajen Najeriya.