Ko me ke haifar da tamowa a Madagascar ?

Mutane a Madagascar suna mamakin dalin da yasa yara basa samun isashshen abinci mai gina jiki-hakan ne ma yasa basa girma kamar sa'aninsu - a yankin mai dubun abinci.

A wata cibiyar gina jiki na al'umma da ke wajen garin Antsirabe, daya daga cikin manyan yankunan Madagascar -wasu yara mata biyu, wadanda suke kasa da shekaru uku da rabi da haihuwa, sun zo domin a duba lafiyarsu.

Idan Jiana da Rova suka tsaya kusa da juna, bambancin na da ban mamaki.

Rova ta fi Jina kajarta sosai. Nauyinta kaso 60 ne kawai daga cikin nauyin Jinan kuma yanayi ta na marasa kwari ne.

Wani ma'aikaci a cibiyar ya na zaton mai yuwa Rova na fama a matsanancin tamowa.

Kamar kasashe masu tasowa a duniya, Madagascar na fama da wannan nau'in tamowar.

Kusan rabin yaran kasar da suke da shekaru kasa da 5 suna fama da ita.

Yakunan masu tsaunuka da ke tsakiyar gari, duk da haka, akwai sarkakiya a lamarin matsanacin tamowa.

Yankin na da albarkar kasar noma inda ake noma nau'ukan abinci daban-daban.

Ma'aunan talauci da tsaftar muhallin kasar basu nuna cewar suna fama da matsaloli ba a kasar kuma suna da kayayyakin aikin asibiti masu kyau.

Duk da haka, wurin mai tsaunuka da ke tsakiyar garin - yankin na Madagaskar wanda ya hada da babban birnin kasar Antananarivo - suna da mafi yawan masu matsanancin tamowa a kasar.

Ko ya aka yi haka ya faru ? ita ce tambayar da masana kamar Simeon Nanama, shugabar hukumar kula da ingancin abinci na asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya ke kokarin ansawa.

'Tamowa mai tsanani'

Yaro yana kamuwa da tamowa ne idan akwai matsanancin rashin abinci.

Yara masu fama da matsakaicin tamowa 'yan sirara ne kuma a wasu lokutan suna da kumburarun tumbi da kaffuwa da hannaye.

Miora Randriamamonjy, mahafiyar Jiana, ta san cewar yaran da suka yi fama da matsanancin tamowa a lokacin da suke yara, ba za su yi kokari ba a makaranta kuma ba za su zamto masu hazaka kamar manya ba. Ko da kuwa yanayin rayuwar ya gyaru daga baya.

Idanun ta sun ciko da hawaye a lokacin da take magana saboda bata da hanyar magance matsalar.

Mr Nananma yana son karin fahimta, ta yadda zai iya agazawa da kudi a wuraren da suka fuskantar matsalar.

Amma ya ce a halin yanzu akwai bukatar su ci gaba da yin bincike. Ya na fatan wani rahoto da ake sa ran zai fito nan da ba da dadewa ba, zai yi karin haske a kan batun.

Kafin nan, akwai bayanai a kan dalilan da suka jawo yawan matsanancin tamowa a yankin mai tsaunuka.