Matashi ya kashe mahaifansa a Enugu

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Matashin dai ya yi amfani da adda ne wajen kisan

Wani matashi da ake kyautata zaton yana da tabin hankali ya yi sanadiyyar mahaifansa da makwabtansu guda tara, a jihar Enugu da ke kudu maso gabashin Najeriya.

An ce dai matashin ya hau iyayen nasa da sara ne da adda, bayan kuma ya kashe su sai ya nemi ashana ya banka wa gidan wuta.

Daga nan kuma sai ya shiga gidan makwabta a inda ya kashe mutane tara da suka hada da kananan yara.

Yanzu haka rundunar 'yan sandan jihar ta Enugu ta baza komarta wajen noman matashin.

Sai dai kuma kwararru kan halayyar dan adam sun ce matashin ba zai rasa tabi ba.