Boko Haram: Nigeria ta kori wani janar

Hakkin mallakar hoto no credit
Image caption Babban hafsan dakarun sojin Nigeria, Janar Tukur Buratai

Wata kotun soji a Nigeria ta sanar da korar wani Janar din soja bisa zarginsa da sakaci a yaki da kungiyar Boko Haram.

Kotun sojin ta sanar da sallamar Brigadiya Janar Enitan Ransome Kuti daga aikin ne bisa sakacinsa har 'yan kungiyar Boko Haram suka kwace garin Baga tare da kwashe dimbin makamai na sojin kasar.

A watan Mayun da ya gabata ne aka gurfanar da Janar Ransome Kuti a gaban kotun sojin da ke zamanta a barikin Mogadishu da ke Abuja tare da sauran sojojin da ake zargi da sakaci a yaki da Boko Haram.

A watan Junairun bana ne dai 'yan Boko Haram suka kai hari a Baga inda suka kwace iko da garin, kafin dakarun Nigeria su kwato garin bayan wasu watanni.

A shekara ta 2013, an kona gidaje kusan 2,000 sakamakon wasu hare-hare a garin Baga mai kan iyaka da jamhuriyar Chadi.