Falasdinawa sun kona kabarin babban malami

Hakkin mallakar hoto Israeli Military Spokesman

Shugaban Faladinawa, Mahmoud Abbas, ya yi tur da hare-haren da wasu Falasdinawa suka kai a kan kushewar da Yahudawa da Kiristoci ke girmamawa.

Mr Abbas ya bayyana konawar da Falasdinawan suka yi wa kabarin babban malamin wanda ake kira Yusuf a matsayin halayya mara kyau.

Ya kara da cewa hukumomin kasar za su sake gina wuraren da aka kona.

Hakan na zuwa ne 'yan sa'o'i bayan da Firai ministan Isra'ila Benjamin Netanyahi ya yi kira ga shugabannin Falasdinawa su kawo karshen hare-haren da ake kaiwa.

Majalisar Dinkin Duniya za ta yi taro domin tattauna wa kan hare-haren da ke faruwa tsakanin Yahudawa da Falasdinawa a 'yan kwanamkin nan, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar a kalla Falasdinawa 30 da Yahudawa bakwai.