'Yar Afrika ta Kudu na shirin 'sayar da' ɗanta

Image caption Matar na fuskantar tuhuma

Wata mata za ta bayyana a gaban kotu a Afirka ta Kudu bisa zargin kokarin sayar da danta da ta tallata a kan dala dari hudu a shafin saye da sayarwa na intanet, watau Gumtree.

Ana sa ran idan matar ta bayyana a gaban kotun majistire ta Pietermaritzburg da ke KwaZulu-Natal kuma za a tuhumeta da safarar mutane.

'Yan sanda sun ce an kama matar mai shekaru 20 a ranar Talata, bayan da wani jami'in leken asiri ya amsa cewa zai sayi yaron.

Yanzu haka an mika dan matar mai shekara daya da rabi ga ma'aikatan kula da jin dadin jama'a.